Monday, 11 November 2019

Ronaldo ya ji haushin canja shi da aka yi bayan da ya kasa cin kwallo

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya cika da haushi a jiya, Lahadi bayan da kocin kungiyar, Sarri ya canjashi bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ya saka Dybala a wasan da suka buga da Milan.Ana ganin Ronaldon be buga wasan da ya kamata ba jiya ba.

Kuma wani abin da ya dauki hankulan a wasan shine, jim kadan bayan saka Dybala sai gashi ya ciwa Juve kwallon da ta zamar mata daya Tilo da ta yi nasara akan Milan.

Ronaldo dai ya bayyana bacin ranshi karara da canja shi da aka yi inda ya gayawa Sarrin wata magana da ba'a san ko me ya ce ba sannan kai tsaye be tsaya ba ya wuce dakin canja kaya ya kuma fice daga Filin wasan kamin a kammala wasan.

Wannan abu da Ronaldo yayi yasa wasu suka caccake shi, ciki kuwa hadda kocin Italy Fabio Capello wanda ya bayyana cewa ta fara karewa Ronaldonne dan kuwa shekaru 3 kenan yaa kasa wuce dan wasa ko daya da kwallo.

Ya kara da cewa ko shine Sarri abinda zai yi kenan kuma Sarrin ya kamata ya gayawa Ronaldon ya rika girmama abokan wasanshi.

Saidai bayan kammala wasan, Sarri ya kare Ronaldo inda yace dan wasan na da rauni a kafa, be kamata ace ya buga wasan ba amma ya tilasta kanshi.

Wannan alamari yasa wasu suka rika wa Ronaldo ba'a, musamman magoya bayan Messi inda har suka rika watsa wannan hoton na kasa dan zolaya.

Wannan dai shine karo na 2 da aka canja Ronaldo tun bayan zuwanshi Juve da abin be mai dadi ba.

Wasu Rahotanni sun tabbatar da cewa, kungiyar ta Juventus ta ce ba zata hukunta dan wasan ba duk da rashin da'ar da ya nuna.

Tuni dai Ronaldo ya bayyana a shafinshi na sada zumunta cewa Lokaci ne da ake fama amma kuma ya ji dadin Nasarar da suka samu.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment