Thursday, 21 November 2019

Ronaldo yayi aure a asirce

Rahotanni daga Italiya sun bayyana cewa tauraron dan kwallon kungiyar Juventus,Cristiano Ronaldo ya angwance a asirce ba tare da an sani ba tare da budurwarshi da suka dade suna tare watau Georgina Rodriguez.Rahotanni daga mujallar Novella 2000 dake kasar Italiya ta bayyana cewa, An yi aurenne a watan Agustan da ya gabata a asirce a kasar Morocco kuma tuni har Ronaldon ya canja tsarin gidanar da lamurranshi inda ya baiwa Matar tashi muhimmanci.

A da dai Mahaifiyarshi ce ke gudanar da dukkan lamurran kasuwancinshi kamin auren amma bayan auten ya karbe wasu abubuwam daga hannun mahaifiyar tashi inda ya damkawa matar tashi.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment