Tuesday, 12 November 2019

SABON BIDIYON SHEKAU: Babu Wani Abu Mai Kama Da Maulidi Da Annabi SAW Ya Yi

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau ya bayyana a wani sabon Bidiyo a jiya.


Bidiyon dai na Mintuna 33 ne, wadda shugaban ya bayyana, ya ke kuma kalubalantar masu yin Maulidin.

Abubakar Sheƙau, ya ce babu wani abu mai kama da Maulidi da Annabi SAW yayi.

Duk da bidiyon ba shi da haske sosai, amma an ga Abubakar Sheƙau rike da wata takarda, wadda a ciki yake karanto hukuncin game da Maulidi.

Bidiyon ya nuna yadda 'yan kungiyar suka galabaita da kuma rashin isassun makamai a wurinsu, wanda hakan ke nuna cewa an ci galabar kungiyar kwarai da gaske.

Shahararren Dan Jaridar nan ne dai ya yi wannan bayani a shafinsa na tiwita, wato Ahmed Salkida.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment