Saturday, 2 November 2019

Sakamakon wasannin Premier League na yau

Kungiyar Manchester United ta sha kashi a hannun Bournemouth da ci daya me ban haushi a wasan da suka buga yau na gasar Premmier League. King na Bournemouth ne ya ci kwallon ana saur a minti 1 a tafi hutun rabin lokaci wanda da dama magoya bayan Man United suka caccaki Aaron Wan Bissaka saboda ana ganin laifinshine.Wannan rashin nasara ta sa Man United ta koma matsayi na 10 da maki 13 bayan buga wasanni 11 wannan itace kakar wasa mafi muni ga Man United tun shekarar 1986/87.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wakilan Man United sun fara tattaunawa da Yariman kasar Saudiyya kan sayen kungiyar da yake son yi.

Arsenal da Wolves sun tashi kunnen doki 1-1 a wasan da suka buga yau wanda Aubameyang ne ya ci musu kwallon wadda daga baya Wolves ta farke ta hannun Jimenez

Kwallon da Aubameyang ya ciwa Arsenal yau itace kwallo ta 50 da ya ciwa kingiyar a wasanni 78 da ya buga mata.

A karo na biyu a kkar wasan bana, Mesut Ozil ya fara wasa da Arsenal kuma bayan wasan yace ya ji dadin buga wasan saidai be ji dadin sakamakon da suka samu ba.

Saidai Kocin Arsenal din, Unai Emery ya bayyana cewa duk da sakamakon marar kyaune amma abinda yayi tsammani kenan.

Liverpool ta buga 2-1 da Aston Villa, Trezeguet na Aston Villa ne ya fara cin kwallo wadda ta so ta makale, sai a minti 87 Robertson ya ciwa Liverpool kwallo ta farko sanna Mane ya ci ta 2 a minti 90 wadda itace kwallo ta 35 da Liverpool taci a cikin mintin karshe a wasa.

Man City ta buga 2-1 da Southampton Aguero da Walker ne suka ci mata kwallayen.

Chelsea ta buga 2-1 da Watford kwallayen da Tammy Abraham da Pulisic suka ci mata.

Brighton ta lallasa Norwich da ci 2-0

Sheffiel ta lallasa Burnley da ci 3-0

Newcastle ta wa West Ham 3-2Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment