Saturday, 30 November 2019

Sarki Sanusi II Zai Yi Sanadin Samar Da Gurbin Karatu Ga Mahaddata Alkur’ani A Wata Jami’a Dake Kasar Dubai

A kokarin sa na ganin an bunkasa ilimi addinin musulunci mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara Jami’ar Alkasimia da ke garin Sharja a hadaddiyar daular larabawa (United Arab Emirate)
In da ya tattauna da mahukuntan jami’ar domin ganin an samar da gurbin karatu ga mahaddata alkur’ani mai girma, wanda hakan zai ba su damar fadada iliminsu.
Ana sa ran wannan jami’a nan ba da jimawa ba za ta samarwa matasanmu masu karatun alkur’ani damar gurbin karatu a wannan jami’a mai koyar da harshen larabci tsantsa.

“Muna da makarantu da mahaddata alkur’ani a Najeriya musamman a jihar Kano wadanda za su iya bayar da gagarumar gudummowa a bangaren alkur’ani da harshen larabci idan suka samu gurbin karatu a wannan jami’a ta Alkasimia.” in ji Sarki Sanusi II

Idan za’a iya tunawa dai Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a baya ya samar da bankin musulunci na Jaiz a yanzu ma yana kokarin samar da wata hanya ta samarwa makaranta alkur’ani da masu koyon harshen larabci gurbin karo karatu don inganta iliminsu.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment