Thursday, 28 November 2019

Naira Dubu 700 ake biyana kudin Fansho>>Tsohon gwamnan jihar Kaduna

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dokar biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho ko alawus na musamman na daruruwan miliyoyin naira.


Tsohon gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya ce N741,000 ake biyansa fansho a matsayinsa na tsohon gwamna.

Ya ce tsoffin gwamnoni a jihar Kaduna, sun amince su karbi fansho daidai da wanda famanan Sakatare ke karba.

Al'amarin ya ja hankali ne bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya nemi gwamnatin jiharsa ta biya shi naira miliyon goma a kowane wata a matsayin alawus na musamman, kamar yadda wata dokar jihar ta tanadar.

Amma a ranar Talata ne majalisar dokokin jihar ta soke ta, tana mai cewa tsoffin gwamnonin jihar kafin shi sun shafe shekaru ba a biya su kudaden ba a zamanin mulkin shi na shekaru takwas.Wasu masana na ganin cewa bai kamata a ci gaba da biyan tsoffin gwamnoni irin wannan kudin ba, idan aka yi la`akari da matsain tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.

Masana irinsu Farfesa Jibrin Ibrahim na ganin fansho na wadanda suka yi aiki ne na tsawon rayuwarsu, ba `yan siyasa ba.

"Siyasa ba sana'a ba ce, don haka don ka yi mulki bai kamata a biya ka fansho ba," in ji shi.

Jihohin Lagos da Gombe da Bauchi da Akwa-Ibom da Kwara da Kano da Rivers na sahun gaba wajen bai wa tsoffin gwamnoninsu kudin alawus na musamman.

Ana biyan tsoffin gwamnonin jihohin daga naira miliyon dari biyu zuwa miliyon dari uku ko ma fiye da haka, bayan kula da lafiyarsu da iyalansu da samar musu gida a Abuja da jiharsu, da sabunta musu motocin hawa bayan shekara uku zuwa shekara hudu ko biyar.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment