Friday, 29 November 2019

Sun Rasa Rayukan Su Kan Hanyarsu Ta Zuwa Bautar Kasa

Wasu dalibai sun rasa rayukansu akan hanyarsu ta zuwa kamfin na bautar kasa.


Daliban dai sun fito ne daga kwalejin kimiyya ta tarayyar Nijeriya dake jihar Kwara.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wasu daga cikin daliban sun rasa rayukan su, yayinda wasu daga cikinsu kuma suka jikkata.

Sai dai babu wani bayani daga mahukunta jahar Kwara, dakuma iyayen wadannan dalibai kan zancen rasuwar daliban.

Daliban dai suna kan hanyarsu ta zuwa jahar Jigawa inda akan hanyar ne hatsarin ya faruwa.

Lamarin dai ya shafi kusan rayukan mutum 16 dake cikin motar.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis zuwa wayewar garin yau Juma'a.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment