Saturday, 9 November 2019

Ta Makance a kokarin canja kalar kwayar idonta

Masu iya magana kance garin neman Gira akan rasa Ido, wannan magana ce ta zo daidai da abinda wata mata yar shekaru 24, Amber Lake ta yi na canja kalar kwayar idonta zuwa Bulu wanda kuma sanadiyyar hakan yasa ta makance.

Amber dai ita a nata lissafin, kurewa kwalliya shine mutum yayiwa jikinshi zane inda tun tana 'yar shekaru 16 ta fara canja kamannin jikinta da zanen da akewa lakabi da Tattoo a turance.

Ta kashe sama da Dala 35,000 wajan wannan zane, kwatankwacin sama da Naira miliyab 12 kenan. Ta sa an yanka mata harshenta gida biyu sannan an karawa kunnenta tsawo.

Sai kuma yanzu da ta mayar da kalar idonta Bulu, sanadiyyar hakan ta samu makantar sati 3, tace a lokacin da ake mayar da kwayar idon nata Bulu, ta ji kamar an farfasa kwalba an watsa mata a cikin idanun.

Ta kuma sha alwashin nan da shekarar 2020 tana so taga ta karade gaba dayan jikinta da zanen inda tace ta lura akwai wasu kananan gurare a kafarta da suka rage basu da zanen.

Ta bayyana cewa wasu da dama suna mata fatan bala'i da zagi da hantara musamman a shafukan sada zumunta inda wasu suka yi fatan inama ace ta makance har abada, wasu kuma suka ce mata mahaukaciya, kai wasu ma fatan mutuwa suka mata.

Saidai tace duk bata mayar da hankali akan irin wadannan kalamai da ake mata dan tasan kowa nada ra'ayinshi, ita dai a ganinta zanen jiki shine kurewa kwalliya inda tace takan mayar da hankaline ga masu yabawa da jinjina mata da kuma bata goyon baya.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment