Thursday, 7 November 2019

Tauraron dan kwallon Juventus ya baiwa Ronaldo hakuri bayan ya yi mai sata

A wasan daJuventus da Lokomotiv Moscow  suka buga jiya, Laraba na gasar cin kofin Champions League wanda Juve tawa Moscow 2-1 wani lamari ya faru tsakanin 'yan wasan Juven, Ronaldo da Aaron Ramsey da ya dauki hankula.
Ronaldo ne ya buga bugun tazara wanda golan Lokomiv Moscow ya ture amma kwallon ta rika Gangara a kan layin  ragar Moscow, wannan yasa Aaron Ramsey ta ida turata cikin ragar kuma shi aka baiwa Kwallon.

Bayan cin kwallonne sai Ramsey yayi wani abu me kama da baiwa Ronaldo Hakuri ganin cewa watakila da ya bar kwallon da ta shiga raga da kanta wadda zata zama ta Ronaldo amma ya turata ta zama tashi,yana ganin kamar ya mai satar kwallone.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment