Tuesday, 12 November 2019

UBA YA YANKA DAN SA, BAYAN YA GANO DAN LUWADI NE

Wani matashi mai shekaru 17 wanda aka bayyana sunan sa da Seran M ana zargin mahaifinsa da kai masa hari saboda ya koma dan luwadi. Mahaifin ya yi masa wannan aika-aika ne a gidansu da ke Central-Western Swiss Canton of Bern.Kamar yadda matashin ya bayyana, ya tashi barci ne ya samu mahaifinsa tsaye a kansa da wuka a makogwaronsa.

Mahaifin da ba a bayyana sunansa ba, ya kira dan nasa da suna dan luwadi kafin ya yanka masa makogwaro da wata kakkaifar wukar, kamar yadda rahoto ya nuna.

Seran, wanda asalin dan kasar Iraqi ne, ya sanar da kafafen yada labarai cewa: "Na kasance mai boye halayyata ta luwadi daga dangina."

Duk da ya san matsayar addininsa akan luwadi, matashin ya ce har yanzu bai ga dalilin da zaisa mahaifinsa kuma musulmi nagari zai aikata hakan ba.

Seran ya yarda cewa sa'a ce kadai ta sa ya kwaci kansa daga hannun mahaifinsa inda ya tsallake katanga ya tsere.

Kafafen yada labaran kasar sun ce makwafta sun kira taimakon gaggawa inda aka kwashi Seran zuwa asibitin Jami'ar Bern sakamakon munanan raunikan da ya samu a makogwaro, kirji, baya da kuma hannayensa.

Seran ya sanar da manema labarai cewa: "Sa a daya da na samu itace, mahaifina bai yi nasarar tsinke babbar jijiyar wuyan ba amma ya raunata makogwarona, sai da aka sa ni suman wucin-gadi a asibitin."

Bayan watanni shida da aukuwar lamarin, matashin na rayuwa a wani bangare daban na Swiss Canton dake birnin Bern, wanda shine birni na biyu mafi girma a kasar.

Sakamakon munanan tabo da ke jikinsa, matashin yace suna tuna masa lamarin sosai.

Seran ya ce: "Ina ganin raunikan a madubi ko kuma idan na dau hotuna, zan kasance dasu har karshen rayuwata."
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment