Tuesday, 5 November 2019

Wani mutum ya mutu bayan cinye kwai kwaya 41

A Jihar Uttar Pradesh wani mutum ya rasa ransa bayan cinye kwai kwaya 41 da aka saka gasar ci tsakaninsa da abokansa.


Subhash Yadav mai shekaru 42 tare da abokansa sun shiga gasa da abokansa ta za a bayar da Rupi dubu 2,000 ga duk wanda ya cinye kwai guda 50 inda a lokacinda ya ci 41 ya rasa ransa.

Yadav ya mutu a lokacinda ya fara cin kwai na 42 wanda nan da nan ya yanke jiki ya fadi, kuma suk kokarin ceton ransa a asibiti ya ci tura.

Mahukuntan asibitin sun ce Yadav ya mutu sakamakon cin kwan da yawa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment