Thursday, 28 November 2019

Wasu sun bullo da sana'ar kama wa mutane layi dan samun kudi

Wasu ma'aurata 'yan kasar Amurka sun yi tayin kama wa mutane layi musamman wadanda suke da sha'awar samun rahusa a ranar garabasar kayayyaki ta Black Friday da farashin kayayyaki ke sauki.


Alexis Granados ta ce mijinta, Steven Velasquez mutum ne mai basirar bullo da dubarun samun kudi.

A cewarta, a baya-bayan nan, mijin nata ya rasa aikinsa a wani kamfanin sake sarrafa kayayyaki.

Ma'auratan na karbar dala 50 domin kama wa mutum layi wanda zai sa su jira a wajen kowane shago a Upland da ke California, kafin ranar ta Black Friday.

Wannan ba sabon abu ba ne sai dai wani tsarin aiki ne na wani don lokaci ba mai tsawo ba.

A shafukan Task Rabbit da Bidvine, wasu shafukan Burtaniya da ke wallafa tallace-tallace na masu aikin yi, mutane suna samun tsakanin £15 da £20 lokaci guda.

A gefe guda kuma, an kirkiri wata manhaja a Amurka domin kawai taimakawa mutanen da ba sa iya bin layi kuma suke da niyyar biyan wasu su kama musu layi.

'Nishadi'
Ana sa ran kimanin mutane sama da miliyan 165 ne za su yi tururuwa zuwa shaguna a Amurka tsakanin Juma'a da Litinin, a cewar hukumar da ke kula da masu sayar da kananan kayayyaki.

Wannan rana ta garabasa a ranar Juma'a, da ta samo asali daga Amurka, inda ake ciniki a lokacin da ma'aikata a Amurkan suke hutu.

Su dai ma'auratan mazauna California sun ce suna aiki domin biyan bukatunsu.

Ba su taba gwada irin wannan sana'a ba amma Alexis ta ce "tana da yakinin wannan ba zai zamo karshe ba saboda a cewarta hanya ce ta samun kudi cikin sauki."
Ma'auratan dai suna da mota inda suke dan hutawa lokacin da suke kamawa wasu layi.

Suna kuma tallata wannan aiki nasu ta kafafen sada zumunta kuma mutane da dama sun nuna sha'awarsu ta son su bi musu layi.

Suna kuma ba kwastamominsu tabbacin samun waje a gaba-gaban layin sannan kuma suka ce idan har abokan huldarsu ba su gamsu ba, ba za su karbi ko Kobo ba.

"Bamu da gida a da, a don haka ba abin takaici ba ne, a cewar Ms Granados tana mai cewa kudi yana da matukar amfani a gare su.

Ma'auratan dai 'yan shekara 20 ne kuma a cewar Ms Granados, wannan kamar sun taka wani mataki ne na gina rayuwarsu.
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment