Monday, 4 November 2019

Wata Babbar Baiwa Da Karama Da Allah Ya Baiwa Marigayi Sheikh Ja'afar

Mafi yawan manyan malaman Sunnah da ke fadin kasar nan, kafin su fara gabatar da Tafseeri sai sun saurari me Sheikh Ja'afar ya fada, ya ya Sheikh Ja'afar ya fassara.


Wannan ba karamar baiwa ba ce da Allah ya yi wa wannan bawa nasa, duk kasancewar babu ko shakka a wancan lokacin, hanyoyin neman ilmi na internet ba su shahara ba kamar a yanzu.

Amma duk da haka Malam ya bata lokacinsa a gun binciken ilmi, wanda yau an wayi gari manyan malaman da ke rayuwa a yanzu (lokacin da ilmi ya kara saukaka a duniyar internet), suna tserereniyar jin fadarsa da ra'ayinsa, wannan baiwa ce daga wurin Allah, wadda kudi, ko mulki, ko sarauta ba sa iya siya maka wannan.

Watarana, na taba taras da wani babban malami da sautin sa ya karade fadin kasar nan, a falonsa, sai na taras da shi yana sauraren tafseerin Malam Ja'afar kafin fara nasa tafseerin.

Allah ya ji kan Malam, ya kyautata makoncinsa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment