Tuesday, 19 November 2019

Wata Budurwa Ta Yi Yunkurin Rungumar Taransifoma Bayan An Yi Mata Auren Dole Da Dan Shekara 70 A Jihar Kano

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata matashiya ta yi yunkurin shiga na’urar da ke bada wutar lantarki wato taransufoma.


Matashiyar ta sanar da mazauna yankin da taransufomar ta ke, cewa an aura mata tsoho ne kuma bata so.

Kungiyar kare hakkin dan Adam karkashin shugabancin Karibu Lawan Kabara ta sha alwashin kwato mata hakkinta.

Al’amarin ya faru ne a ranar Juma’a da ta gabata, 15 ga wannan watan da muke ciki na Nuwamba.

 Wata matashiya ce ta yi yunkurin shiga cikin na’urar da ke bada hasken wutar lantarki wato taransufoma.

Wannan lamari dai ya faru ne a unguwar Sharada da ke yankin karamar hukumar birnin Kano bayan da ta yo tattaki tun daga unguwar Rimin Kebe da ke yankin karamar hukumar Ungogo.

Daya daga cikin wadanda suka kaiwa matashiyar dauki yace, ta samesu da koken cewa an yi mata auren dole ne da wani tsoho da bata so. A don haka ne take bukatar mafita.

Mazauna yankin sun kara da cewa, tana gama fada musu hakan sai ta nufi dakin da na’urar bada wutar lantarkin ke ciki don kawo karshen rayuwarta. Sai dai sun yi gaggawar hana ta shiga.

Ganin wannan yunkurin ne yasa kungiyar kare hakkin dan Adam ta shiga lamarin. 

Shugaban kungiyar, Karibu Lawan Kabara, ya bayyana cewa zasu yi iyakar bakin kokarinsu wajen ganin sun kwato wa matashiyar hakkinta.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment