Sunday, 3 November 2019

YA KAMATA DUNIYAR MUSULUNCI TA JI WANNAN LABARIN

Na saurari cikakken rahoton da Freedom FM Kano ta wallafa akan tona asirin wani Malamin addinin Nasara da ya gina wani katafaren sansani a wani babban jeji a birnin Benin Jihar Edo yana ajiye 'yan gudun hijira wanda annobar ta'addancin Boko Haram ya kore su daga garuruwansu.


Malamin addinin nasaran mai sunan Solomon Fuloroshun ya bude sansanin ne tun a shekarar 1990, yana samun tallafi kai tsaye daga manyan majami'u na kasashen waje, a lokacin da yakin Boko Haram ya yi kamari, sai ya dinga aikawa Maiduguri ana kwaso masa yaran musulmai ana kaisu sansaninsa a jihar Edo.

Binciken kwakwaf na kamfanin dillancin yada labarai na AFP ya nuna cewa yanzu haka akwai yaran musulmai maza da mata sama da dubu hudu (4000), da mata zawarawa wadanda aka kashe mazajensu a rikicin Boko Haram sama da dari hudu (400) a sansanin, wadanda duk an kwaso su ne daga Maiduguri da sassan arewan Nigeria, kuma duk an canza musu addini daga musulunci zuwa addinin Nasara.

A hiran da akayi da wasu mata da suke sansanin gudun hijran, sun bayyana cewa Malamin addinin Nasara bayan ya tilasta musu kafurci, yana zaban kyawawa daga cikin matan yana musu fyade, duk wacce taki amincewa yayi mata fyade yana mata dukan tsiya har sai jikinta ya yi jini.

Wani jami'in tsaro da ake hira dashi wanda ya bukaci a buye sunansa, ya bayyana cewa aiki ya kaisu cikin sansanin a jihar Edo, ya shaida komai da idonsa, halin da yaga yaran Musulmai a ciki ta hanyar canza musu addini da rayuwa kuma suna yaren Hausa radau a bakinsu hakan yayi matukar tayar masa da hankali.

Akwai cikakken rahoton na Freedom FM a audio zan sakashi a group WhatsApp domin a saurari cikakken bayanin

InnalilLahi wa innaa ILAIHI RAJI'UNN hakika wannan al'amari mai matukar tayar da hankali ne, wannan shine sakamakon aikin da Muhammad Yusuf shugaban Boko Haram na farko ya yiwa makiya addinin Musulunci, wanda munsha bayyanawa a baya cewa ta'addancin Boko Haram kwangila ne domin a yaki Musulunci da Musulmai a Arewan Nijeriya. 

Yaa Allah Ka rufa mana asiri, Ka tsaremu, Ka haramtawa makiyanmu samun nasara a kan mu Amin
Datti Assalafy.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment