Tuesday, 12 November 2019

Ya Kulle Kanwarsa A Daki Na Tsawon Shekara Biyu A Rigasar Jihar Kaduna

HUKUNCI KO AZABTARWA?

Shugabar Kungiyar ARRIDA RELIEF FOUNDATION dake Kaduna Hajia Rabi Salisu ita ce ta gano wannan baiwar Allah tare da yunkurin taimaka mata.


Gaa bayanin Hajia Rabin kamar haka;

Wannan ita ce Hassana wacce yayanta ya kulle ta tsawon shekara biyu a daki a yankin Rigasa dake jihar Kaduna.

Dalilin kawai shine domin wai ta dage sai ta koma dakin mijinta, wato uban 'ya'yanta hudu wanda daginta suke zargin ba ya son ta kuma ya sake ta, shi ya sa ta sami damuwa wato (Depression) 

Dalilin haka shine suka yi mata wannan danyen hukunci na kulle ta cikin daki wanda yashi ne cikin sa babu ko siminti balle tabarma. A nan take bayan gari da fitsari. Haka bacci da cin abinci duk a cikin wannan yanayin. 

A jiya 11/11/19 Kungiyar ta ARRIDA RELIEF FOUNDATION ta ceto Hassana kuma yau ake sa ran za su kai ta asibiti domin nema mata lafiya.

Da haka shugabar Kungiyar ta ARRIDA RELIEF FOUNDATION ke kira ga sauran kungiyoyi da su shigo cikin wannan lamarin domin taimaka mata.

Za a Iya tuntubar Hajia Rabi domin karin bayani 07034372027Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment