Wednesday, 27 November 2019

Ya Rabu Da Matarsa Saboda Ta Aibanta Buhari

"Zan iya rabuwa da kowa amma ba zan iya rabuwa da shugaba Buhari ba, hakan ya sanya na iya rabuwa da mata ta, wadda akalla mun kai tsawon shekaru sama da 30 muna rayuwar aure, ba tare da wata matsala ba", inji wani Dattijo mai suna Jumare Bulama dan asalin jihar Katsina mazaunin karamar hukumar Dabai dake jihar Katsina.


Dattijon ya yi fice wurin son Buhari, har yana ikirari kan Buhari zai iya rabuwa da kowa a rayuwar sa amma banda Shugaba Buharin.

Rahoton namu ya kara da ce mana" Ita dai matar mai suna Hajara Abdullahi Giwa tace! Wani abu bai taba hada su da mijin na ta ba a tswon rayuwar su na aure da har zai sake ta.

Amma daga bisani an tabbatar mana cewa" shi dattijon Jumare Bulama, yayi ikirarin saki daya rak ya yi wa matar kuma ko a yanzu kofa a bude take na dawowa da matar sa domin suci gaba da zaman aure.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment