Tuesday, 5 November 2019

Yadda Abokanan Makarantar Shugaba Buhari Suka Karrama Ministan Jiragen Sama, Hadi Sirika

A ranar Asabar din da ta gabata ne, Abokanan Makarantar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari 'yan shekarar 1953 a Katsina Middle School, suka karrama Sanata Hadi Sirika, Minista jirage na Nijeriya, saboda irin guddummuwar da yake bayarwa wajen cigaban Nijeriya da kuma jihar Katsina.


Taron karrammawar da walimar ya gudana ne a dakin taro na liyafa palace hotel da ke kan hanyar Kano cikin birnin Katsina.

Da yake jawabi a madadin sauran yan ajin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Sanata Abba Ali ya bayyana dalilan da yasa suka karrama Sanata Hadi Sirika da cewa mutum ne Mai Jajircewar gaske a duk aikin da shugaban kasa ya Sanya shi, da Kuma gagarumin cigaban da ya kawo a fanni Jiragen Sama kasar. Kamar irin gyara da daga martabar filin sauka da tashi na Nmandi Azikwe da ke Abuja cikin dan kankane lokaci aka kammala aikinsa.

Abba Ali ya Kara da cewa a jihar Katsina, irin yadda ya taimakawa matasanmu da ayyukan yi a jihar Katsina, Wanda tunda aka yi jihar Katsina, ba mu taba samun Ministan da yaba Matasa mu aikin yi ba kamar shi. Shi ya sa Yan ajin muka ga ya dace mu karrama shi, Saboda duk wanda ya yi abun yabo, ya kamata a yaba mashi domin kara bashi kwarin gwiwa cigaba da ayyukan alheran da ya faro a Zango da ya gabata. Ya Zama tilas ne mu yaba mashi a matsayinmu wadanda suka zauna aji daya da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Shima da yake maida jawabin, Wanda aka karrama din Kuma Ministan Harkokin Jiragen Sama Nijeriya, Sanata Hadi Sirika ya bayyana jin dadinsa bisa ga wannan karramawa da Abokanan Makarantar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suka yi mani Kuma ba Zan taba mantawa da wannan karamci da wadannan mutane masu daraja suka yi Mani ba.

Sanata Hadi Sirika ya kara da cewa yau wadannan dattawa, suna karrama ba Dan siyasa ba, Saboda a gabansu aka haife mu, suka Yi Mana tarbiyya har muka kai wannan matsayi. Har ila yau, daya daga cikin su ne, ya ke Shugaban Kasa Tarayya Nijeriya a yanzu, wanda muke aiki da shi. Irin wadannan mutane masu daraja ko buda baki su ce Allah Sam barka abu ne Mai tasiri sosai. 

Hadi Sirika ya cigaba da cewa ba ni da kalmomin da zan yi amfani da su don in mika godiyata ta musamman gare su Kuma in jadadda masu cewa kujera irin ta mulki, kujera ce Mai shudewa, kamar gobe ne zaa ce na taba yin minista. Amma irin ayyukan da Zan yi su ne za su zama hotuna bayan bani bisa, shi yasa babu hotona a maaikatun da suke karkashina. Shi yasa nake bakin kokarina Kuma muke hadawa da addua. Godiyata ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bani dama ta daya, Kuma ya Kara bani ta karo na biyu, Allah ya Kara mashi lafiya.

Taron ya samu halartar yan uwa da abokan arziki, babban Jojin Jihar Katsina, Mai Sharia Musa Danladi Abubakar, Sayyu Dantata, Abokanan tafiyar siyasar Sanata Hadi Sirika na Kananan Hukumomi talatin da hudu dake Jihar Katsina.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment