Saturday, 9 November 2019

Yan Boko Haram na rike da wasu kananan hukumomi biyu a Najeriya

Wasu rahotanni daga kungiyoyin dake sa ido dangane da batutuwa da suka jibanci ayukan jinkai a Najeriya sun gano cewa akalla mutane milyan 1 da dubu 200 ne Boko Haram suka yi wa kafar-rago, a cikin kananan hukumomi biyu a Jihar Barno.Al’umomin yankunan da lamarin ya shafa ,na cikin wani halin rashin tabbas dangane da batun tsaro, hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da hukumomin kasar ke ci gaba da bayyana cewa suna daf da kawo karshen kungiyar Boko Haram. Banda haka a dan tsakanin nan yan kungiyar ta Boko Haram sun kai wasu jerryn hare-hare tareda kisan sojojin Najeriya.

To domin ji yadda masana ke kallon rahoton Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Khalifa Dikwa, masanin tsaro a najeriya, ga kuma yadda hirarsu ta kaya .Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment