Wednesday, 6 November 2019

'Yan sanda sun ceto yara da mata fiye 200 a Ibadan

Jamai'an tsaro na farin kaya da 'yan sanda ne dai su ka yi wa gidan kawanya inda suka samu yara da mata cikin shiga irin ta musulunci cikin yanayin yunwa da kishirwa.


A lokacin samamen dai jami'an tsaron sun kama mai gidan 'azabtarwar' Alfa Ismail Olore tare da mataimakansa guda takwas inda kai su sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincikeJami'an tsaron sun kama mutum 45, inda kuma suke ci gaba da samame domin kama duk wanda yake da hannu a al'amarin.

An samu mutum fiye da 200 a gidan Alfa da suka hada mata da kananan yara.
To sai dai Alfa Isma'il ya shaida wa jami'an tsaro cewa suna koyar da Alkur'ani kuma mahaifa da 'yan uwan mutanen ne suke kai su.

Ya ce "dukkan wadanda suke tsare a cikin wannan gida iyayensu ne suka kawo su garemu domin a yi masu magani.

"Da yawa daga cikinsu miyagun kwayoyin da hodar ibilis da tabar wiwi suke sha. Amma babu wanda muka sanya wa sarka ko mari sai dai muna yi masu addu'ar rokon Allah da ayoyin Alqur'ani ne".

Wani wanda ya shaida abin da ya faru ya shaida wa jami'an tsaro cewa "Yanayin da yaran suke ciki ya nuna sun galabaita, ga kuma alamar yunwa da kishirwa a jikinsu; wanda ko a lokacin da aka kawo musu ruwan sha na ledan nan da ake kira pure water sai suka yi ta wawar dauka domin su sha."

Wannan samame na zuwa ne kwanaki biyu bayan rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta kama wani malamin coci, Sunday Joseph Ojo da wasu mutum 10 inda suke da wani sansani da aka samu ceto yara 15 da ke cikin mari.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment