Thursday, 28 November 2019

Yan Ta'adda Sun Sake Ajiye Makamansu A Jihar Zamfara

A cigaba da yunkurinta na samar da zaman lafiya a jahar Zamfara, wanda ya sa gwamnatin jahar ta bullo da shirin sasanci, wanda ya ke cigaba da samun nasara. 
A yau gwamnan jahar Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya karbi Makamai dangin bindigogi, Albarussai a hannun tsofaffin 'yan bindigar da su ka rungumi sulhun kuma su ke cigaba da Mika mukamansu.

Da ya ke jawabi Mai Daraja gwamnan jahar, Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya nuna matukar jin dadinsa ga yadda wadannan tsofaffin 'yan bindigar ke baiwa Shirinta na sulhu goyon Baya Wanda ya Kai ga bayan sun Mika wuya, ta hanyar dena kisan dauki daidai, garkuwa da mutane da kuma satar shanu, yanzu sun fara Mika mukamansu ga gwamnatin jahar.


Haka zalika gwamnan ya kara kira ga duk wani mai ta da kayar baya tun ba na cikin dazukka kawai ba da su Mika wuya, domin samun zaman lafiya Mai dorewa, a jahar 

Taron karbar makaman dai ya samu halartar Kwamishin 'yan Sanda na jahar Zamfara, Usman Nagwaggo, Babban mai baiwa gwamna shawara Akan sha'anin tsaro Hon Abubakar Dauran Justice  da Sauran Manyan makaraban gwamnatin jahar Zamfara.

 ABDULMALIK SAIDU MAIBIREDI
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
28th November, 2019Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment