Friday, 8 November 2019

'Yan wasa 7 da Man United ke shirin saye

A yayin da ake kusa da bude kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa a watan Janairu, Rahotanni tuni suka fara fitowa akan yanda kasuwar zata kasance, Evenin Standard ta ruwaito 'yan wasa 10 da Man United Zata Siya a watan Janairun.Man United dai na fama da rashin nasara a wasannin da take na gasar Premier League a bana inda a yanzu haka take matsayi na 10 a kan teburin Premier.

'Yan wasan da Kocin kungiyar, Ole Gunner ke son saye sune kamar haka, Tsohon dan wasan Liverpool, Emre Can, sai Richarlison na Everton, sai matashin dan wasannan na Red Bull, Braut Haaland.

Sauran sune, Moussa Dembele na Lyon da Mario Mandzukic na Juventus, Jadon Sancho da James Madisso.

Akwai kuma Kai Havertz da shima akace sun fara magana da Man United.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment