Saturday, 9 November 2019

Yanda Wasannin Premier League na yau suka kasance

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sha kashi a hannun Leicester City da ci 2-0 a wasan da suka buga yau na gasar cin kofin Premier League inda Jamie Verdy da James Madisson suka ciwa Leicester kwallayenta.
Da wannan nasara, Leicester City ta zama ta biyu akan teburin na Premier League inda Arsenal ta koma ta 6 da maki 17. Kocin Arsenal, Unai Emery ya bayyana cewa shine abin zargi dan kuwa 'yan wasan nashi sun yi abinda ya gaya musu saidai yace suna bukatar a kara hakuri da su.

Da aka bayyanawa Emery cewa rashin nasarar da yayi a wasanni 50 sun fi muni fiye da wasanni 50 na karshe da tsohon kocin kungiyar, Wenger yayi sai yace adai kara hakuri dasu.

Chelsea ma ta ci 2-0 a wasan da suka buga yau ita da Crystal Palace inda Tammy Abraham da Pulisic suka ci mata kwallayen 2.

Da wannan kwallo da Tammy Abraham yaci yawan kwallayenshi suka zama 10 daga wasanni 12 da ya buga kuma shine dan wasa mafi karancin shekaru, 22 bayan Arjen Robben, 21 da yaci wa Chelsea kwallaye 10. Da wadannan yawan kwallaye kuma Tamy Abraham ya kafa iri  tarihin dan wasan Man United, Marcus Rashford inda yaci kwallaye 10 a  wasanni 33 da ya buga a kakar wasan data gabata.

Chelsea yazu ta koma matsayi na 3 bayan wannan nasara. Wannan itace nasara ta 6 da Chelsea ta yi a jere. Saidai dan wasanta, Pulisic ya ji rauni.

Tsohon dan wasan Chelsean, Gary Cahill da ya koma Crystal Palace a yau ya buga wasa a gidan Chelsean karon farko tun bayan barinta. Kuma wata bajinta da yayi wajan tare kwallon da Willian ya so ya ci ta jawo mai yabo wajan magoya bayan Chelsea. Kocin Chelsean, Lampard ma ya gaisa sosai da Cahill bayan wasan.

Sauran wasannin Premier League da aka buga yau sune, Tottenham da Sheffield sun buga 1-1, Everton ta ci Southampton 2-1, Necastle ta ci Bournemouth 2-1 sai Sai Burnley da ta ci West Ham 3-0.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment