Tuesday, 12 November 2019

Yanda wata Mata ta kunyatar dani ta hanyar runguma da sumbatata>>Ali Nuhu

A hirar da yayi da jaridar Punch, Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki ya bayyana avu mafi bashi kunya da masoyanshi mata suka mai.
Ali ya bayyana cewa na farko suna kasar Saudiyya shi da matarshi sai ga wata wata mata ta zo ta baiwa matar tashi waya tace ta daukesu hoto.

Ali ya kuma bayyana cewa akwai ranar da a Abuja ya fito daga shagon siyayya wata ta rungumeshi ta kuma sunbace shi hakan ya kuma sake faruwa dashi a Dubai, Ali yace ta ji kunyar wannan abu sosai.

Yace bazai yadda ya fito fim tsirara ba ko nawa za'a bashi hakanan ba zai fito fim a matsayin dan luwadi ba kuma ba zai fito fim din da ake soyayyar taba jiki da yawa ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment