Saturday, 9 November 2019

Yawaitar Satar Yaran Kano : Sarkin Bichi ya je Rangadi Jihohin Inyamurai domin ceto Yaran da aka Sace

Mai martaba Sarkin Bichi Alh Aminu Ado Bayero ne yake rangadi a jihohin Kudu maso gabas (jihohin Inyamurai). Inda yake tattataunawa da gwamnonin jihohin da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro don ganin an kwato ragowar yaran da aka sace daga jihar Kano aka kai su yankunan Inyanurai.


Sarkin na Bichi ya fara ziyarar tasa ne a ranar Alhamis 7 ga Nuwamba. Inda ya ziyarci Gwamnan jihar Enugu. Inda bayan kamalla tatttaunawa da Gwannan, Sarkin ya gana da jamian tsaro.


Bayan kamalla ziyarar jihar Enugu, Sarkin ya ziyarci jihar Imo Inda ya tatttauna da Gwamnan Imo Mr Emeka Edohoha a fadar gwamanatin jihar. Bayan kamalla tattaunawa, Sarkin Bichi ya kuma tatttauna da jami'an tsaro akan batun satar yaran.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment