Thursday, 5 December 2019

AISHA BAKARI GOMBI: Mace Jaruma Da Ta Addabi Mayakan Boko Haram A Jihar Adamawa

Tahiri ya nuna cewa mayakan Boko Haram dake jihar Adamawa suna tsoron Aisha fiye da jami'an Gwamnati. 
Aisha dai an haife tane a garin Gombi dake jihar Adamawa, kafin zuwan rikicin Boko Haram ta kasance 'yar farauta mai farautar namun daji, amma tunda rikicin Boko Haram ya shigo garinsu ta sadaukar da rayuwar ta don al'umma su zauna lafiya. 

Aisha ta nemi tallafin kudi don sayen bindiga amma ba ta samu ba, a karshe kawai ta sayar da keken ta na dinki don sayan bindiga don  amfani da ita wajen yaki da Boko Haram.

Aisha a matsayin ta mace mai shekaru 38, ta jagoranci daruruwan mazaje wajen yaki a lokacin da gwamnatin jihar Adamawa ta dauke ta cikin 'yan civilian JTF masu yaki da Boko Haram.

Aisha da matar aure ce wanda Allah ya azurta da 'ya 'ya bakwai (7).

Daga Bangis YakawadaKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment