Tuesday, 3 December 2019

ALBISHIR GA 'YAN NIGERIA: An Cimma Matsaya Game Da Kudin Data

Bayan doguwar tattaunawa da kamfanonin sadarwar Nigeria suka yi, MTN, Airtel, Glo da 9mobile game da umarnin rage kudin sayan data daga kamfanonin sadarwar, kamfanonin sun cimma matsaya game da sabon farashin datan.


Shugaban hukumar kula da harkokin sadarwa  (NCC) Farfesa Umar Danbatta ya mika wa Ministan sadarwa Sheikh Isah Ali Pantami tsarin da kamfanonin suka tsara, sai dai ba'a karanta sabon tsarin a fili ba zuwa yanzu, nan gaba kadan za'a bayyana sabon tsarin da kuma lokacin da za'a fara zartas dashi Insha Allah.

Maigirma Ministan Sadarwa Dr Isah Ali Pantami yace "Kudaden sayar da Data a Nigeria yayi yawa, kuma yana jawo koma baya wa harkar, abinda zai kawo cigaba wa harkar sadarwa shine data din yayi araha, hakan zai fi jawo hankalin mutane zuwa ga sayan datan, su kansu kamfanonin zasu fi samun kudi idan datan yayi araha, tsadar sa kuma zai kore mutane daga sayan datan, wanda hakan koma baya ne..." Inji Maigirma Ministan Sadarwa.
Daga Datti Assalafiy.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment