Monday, 2 December 2019

Aminu Dantata ya bayar da tallafin Miliyan 50 ga Ilimi a Kano

Attajirin dan kasuwarnan na Birnin Kano, Alhaji Aminu Dogo, Dantata ya bayar da tallafin Naira Miliyan 50 ga sakandiren makarantar mata dake Dala Kano.Me taimakawa gwamnan Kano kan harkokin kafafen sada zumunta, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka ta shafinshi na Twitter inda ya ce hakan na cikin kiran da gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi ne na shigar jama'ar gari kan harkokin Ilimi.

Ya kara da cewa cikin tallafin da Dantata ya bayar akwai Bandaki guda 10 da kuma Riyoyin burtsatse 5 dan tallafawa karatun yara mata a Kano.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment