Tuesday, 3 December 2019

An fi samar da ayyukan yi a kudancin Najeriya, Kuma talakawa zasu karu idan Gwamnati bata dauki mataki ba>>Bankin Duniya

A sabon rahoton dan bankin Duniya ya fitar ya gargadi mahukuntan Najeriya akan su dauki matakan kirkiro da hanyoyin samar da kudin shiga na cikin gida da kuma samar da ayyukan yi idan kuwa ba haka ba to talauci zai karu sosai a Najeriya.
Rahoton yace a yanzu haka akwai kimanin mutane miliyan 100 dake cikin talauci dake rayuwa kasa da dalar Amurka 1.90, kimanin Naira 685.5 kenan a kowace rana kuma kaso 80 cikin 100 da wadannan mutanen suna yankin Arewane.

Rahoton yace akwai kuma matsalar karuwar jama'a fiye da yanda ake samun habakar tattalin arziki a Najeriya inda yace daga yanzu zuwa shekarar 2020 da 2021 ana sa ran tattalin arzikin Najeriya zai karu zuwa kaso 2.1 amma kuma yawan jama'a zai karu zuwa 2.6 duk shekara.

Rahoton ya bayar da shawarar cire tallafin man fetur da kuma cire shamakin kasuwanci da samar da ayyukan yi inda tace idan ba haka ba nan da shekarar 2030 za'a samu karin talakawa a Najeriya zuwa miliyan 30 wanda zai zama kaso 25 cikin 100 na talakawan Duniya baki daya kenan.

Rahoton ya kuma labarto cewa yawanci anfi samar da ayyukan yi da abubuwan habakar tattalin arziki a yankunan tsakiya da kudancin Najeriya inda ake barin Arewa a baya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment