Tuesday, 3 December 2019

An gano Makarantar koyar da damfara ta Yanar Gizo a Najeriya

EFCC ta gano wajen da ake bai wa masu zambar intanet horo a Najeriya

Jami'an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gano wani gini da wasu da ake zargin masu zamba ta intanet ne suke amfani da shi wajen bai wa mutane horo kan yadda za su kware a harkar zambar intanet. 


Wajen yana kauyen Ikot Ibiok da ke karamar hukumar Eket ne ajihar Akwa Ibom akudancin Najeriya. A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwajaren ya fitar, ta ce an kama wadanda ake zargin masu zamba ta intanet ne har 23.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment