Tuesday, 10 December 2019

An kori Dan kwallon Najeriya daga kungiyar da yake kwallo a Turai bayan daya Dirkawa diyar shugaban kungiyar ciki

Wani Rahoto daga ghanaScoocer.net ya ruwaito cewa wani matashin dan kwallon Najeriya da ba'a bayyana sunanshi ba dake wasa a wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Slovenia ya dirkawa diyar shugaban kungiyar ciki wanda kuma hakan ya jawo aka koreshi daga bugawa kungiyar kwallo.Rahoton yace tuni dan kwallon har ya dawo Najeriya.

Da yake bayyana yanda abin ya faru, yace Budurwarshi wadda diyar shugaban kungiyarce ta gaya mai cewa ta na ciki kuma nashine, labarin ya kai kunnen mahaifinta.

Yace daga nanne sai aka kirashi aji ta bakinshi inda ya tabbatarwa da masu gudanarwar kungiyar cewa ciki  nashine, daga nan sai aka dakatar dashi. Yace daga baya ya samu labari daga wakilinshi cewa an koreshi daga kungiyar.

Yace abin ya bashi mamaki dan kuwa shi da yarinyar duk sun mallaki hankalin kansu kuma zasu iya yin abinda suke so. Yace wakilinshi yace zai kai kara zuwa hukumar kwallo ta Duniya FIFA dan a bi mai hakkinshi. Dan kwallon yace ya rattabawa kwantirakin yiwa kungiyar wasa na tsawon shekaru 3 hannu hadda damar karin shekara 1 kamin wannan lamari.

Yace abin takaici ma shine yanzu sun tursasawa budurwar tashi ta daina magana dashi a shafukan sada zumunta sannan sauran abokan wasanshi ma a kungiyar basa son magana dashi akan busurwar tashi, bai san yanayin da take ciki ba.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment