Wednesday, 4 December 2019

Atiku Ya Maka Hadimar Buhari A Kotu, Ya Nemi Ta Ba Shi Diyyar Naira Bilyan 2.5

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya rattaba hannu akan takardar kara tsakanin shi da hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mai suna Lauretta Onochie, inda Atiku yake neman kudin diyya naira bilyan Biyu da milyan biyar bisa abunda ya kira bata mishi suna da Lauretta ta yi. 


Atiku na tuhumar Onochie ce da zargin bata masa suna, inda ta wallafa wasu bayanai a shafin ta na Twiter a lokacin zaben shekarar 2019, inda take cewar 'Jami'an tsaro a kasar Dubai suna bibiyar Atiku, kuma ya tafi gabar ta tsakiya ne don siyo yan ta'adda.

Atiku yace tun a lokacin faruwar hakan sun rubutawa Onochie wasika akan ta nemi afuwa sannan ta janye kalaman ta, amma tayi kunnen uwar shegu ta cigaba da yada kalaman batanci akansa. Atiku ya bayyana kalaman na Onochie a matsayin shaci-fadi da tsagoran karya, inda ya nemi kotu ta takawa Onochie birki daga aibanta shi.
Daga Haji ShehuKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment