Thursday, 12 December 2019

Ba zaki Zo Kano ki mana abinda kika yi a Kaduna ba Kafa a Bude>>Musa Mai Sana'a ya gayawa Jarumar fim din Hausa

Tauraron fina-finan Haus, Musa Mai Sana'a ya caccaki wata Jaruma da bai bayyana sunan ta ba inda yake gugar zana ta hanyar yiwa abokin aikinshi, Ibrahim SharuhKhan fadan cewa yaki gayawa 'yar uwarshi gaskiya.A cikin bidiyon da duń∑a jaruman biyu suka wallafa a shafukansu na Sada zumunta, Musa Mai Sana'a ya bayyana cewa, tayi Birthday a Kaduna, ta yi a Abuja ta yi a Jos, ba zata zo Kano ta mana ba, Kano garin bayin Allah ne kuma ba zamu yi shiru a rika wa jaruman Fim kudin goto ba.

Mai Sana'a ya kara da cewa, ba za su hana mutum yin abinda yake so ba amma idan yayi ba daidai ba dole zasu fada.Rahama Sadau dai ta saka wata Jar Riga a wajan bikin murnar zagayowar ranar Haihuwarta da kuma na bude gidan Abincinta da kafarta daya take a waje inda hotunan suka jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta.

Kalli Bidiyon na Mai Sana'a a kasa:


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment