Wednesday, 4 December 2019

Ba zamu amince da dokar kalaman kiyayya ba>>Shugaban majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal

Shugaban majalisar Dattijai,Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa majalisar ba zata amince da dokar kalaman batanci dake gabanta inda yace zasu yi abinda al'umma ke so.Dokar ta jawo cece-kuce sosai a ciki da wajen Najeriya inda wasu ke zargin cewa za'a yitane dan hana jama'a fadar albarkacin bakinsu,wasu kiwa zargi suka yi cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai yi amfani da wannan doka dan samun zarcewa a karo na 3 akan mulki zargin dukka aka yi watsi dasu.

Sanata lawal ya mayar da martanine ga wasikar da kungiyar dake ikirarin kare hakkin al'umma ta Najeriya ta aikamai inda tace daya daga cikin ginshikan dimokradiyya shine 'yancin fadar albarkacin baki da sharhi akam al'amuran gwamnati kuma wannan doka da suke shirin yi zata taiwa 'yancin fadar Albarkacin bakin karan tsaye.

Lawal yace ba zasu amince da duk wata doka da zata keta hakkin 'yan kasa ba inda yace zasu saurari abinda 'yan kasa ke so.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment