Tuesday, 3 December 2019

Babu ranar bude iyakokin Najeriya>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa be bayar da ranar da za'a bude iyakokin kan tudu na Najeriya ba.Shugaban ya bayyana hakane a gidanshi dake Daura jihar Katsina yayin da wasu dattawan jihar ta Katsina suna kaimai ziyara har gida. Ya kara da cewa rufe iyakokin ya rage amfani da man fetur da sama da kashi 30 cikin 100.

Yace watanni 2 bayan rufe iyakokin dan hana shigo da wasu kayayyaki musamman shinkafa gwamnati na amfani da hakan dan farfado da ayyukan noma.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment