Sunday, 1 December 2019

Dan wasan Najeriya ya taimakawa Leicester City komawa matsayi na 2 a Teburin Premier League, Arsenal kuwa bata cannja Zani ba

Tauraron dan kwallon Najeriya dake bugawa Leicester City wasa, Ihaenacho ya taimakawa kungiyar yin nasara a wasanta na yau inda ya bayar da taimako aka ci kwallo ta farko sannan shima ya ci kwallo ta 2.Wannan masara ta baiwa Leicester Damar komawa matsayinta na 2 a teburin Premier League da maki 32 bayan da Man City ta dana matsayin daga jiya zuwa yau.

Wasan da Arsenal ta buga da Norwich City ya kare da sakamakon 2-2 wanda ana iya cewa bata canja zani ba kenan duk da korar da Arsenal tawa kocinta, Unai Emery.

Itama dai Manchester United 2-2 ta buga da Aston Villa a ci gaba da fama da rashin nasara da take yi a 'yan kwanakinnan.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment