Wednesday, 4 December 2019

Fada tsakanin Hausawa da Yarbawa yayi sanadin mutuwar mutane 3 a jihar Osun

Wani rikici daya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a kauyen Iyere dake karamar hukumar Atakumosa ta Yamma dake jihar Osun.Rahoton jaridar Punch yace wani bafulatani da Bayarbe suke fada sai wani bayerabe ya zo rabasu, daga nanne sai tsautsai, wanda yazo rabon fadan ya mutu.

Nanne fa sai matasan Yarbawa a kauyen suka kashe Hausawa 2 a wajan daukar fansa sannan kuma aka kona shaguna da dama mallakar Hausa da Fulani a kauyen.

Saidai hukumar 'yansandan yankin sun bayyana cewa mutum daya ne ya rasa ransa a rikicin.

Basaraken yankin,Samuel Falaye ya tabbatar da cewa, an samu rikici kuma an tlrasa rayuka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment