Monday, 2 December 2019

Ganduje ya aika wa majalisa sabon kuduri kan sabbin masarautu

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aikawa da wani sabon kudiri ga majalisar jihar, domin kafa sabbin masarautu.


Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta jihar ta sake aika wani sabon kudiri da zai bayar da damar kafa masarautar Rano da Gaya da Bichi da kuma Karaye.Kwamishinan ya bayyana cewa an gyara kudirin dokar masarautu ta 2019 ne saboda gyaran ya shafi jama'a.

Barista Ibrahim Mukhtar shi ne lauyan bangaren gwamnatin jihar, kuma ya shaida wa BBC cewa kotu ta yanke hukuncin ne ba tare da tsayawa ta yi bincike yadda ya kamata ba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment