Sunday, 1 December 2019

Gwamna Zulum Ya Ziyarci Kauye Mafi Hadarin Boko Haram A Jihar Borno

Maigirma gwamnan jihar Borno kuma Buharin Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Marte gari mafi hatsari a jihar Borno, garin da ya kasance babban sansanin kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP da suke rike da ikon garin na tsawon lokaci.
Tun bayan wanzuwar ta'addancin Boko Haram shekaru kusan 10 da suka gabata, sai yanzu aka samu wani shugaba farar hula da ya iya taka kafarsa a garin Marte saboda kusan garin gaba daya yana karkashin ikon Boko Haram/ISWAP ne.

Marte yana yankin tafkin Chadi inda ISWAP ke wanzar da ayyukanta na ta'addanci, hatta kisan shugaban ISIS Abubakar Al-baghdadi da gwamnatin Amurka tayi, manyan kwamandojin yakin ISWAP sai da suka hadu a garin Marte suka masa salatul gha'ib ba da jimawa ba.


Wallahi nayi mamaki matuka da na ga gwamna Babagana Umara Zulum ya iya taka kafarsa a garin saboda gari ne mai matukar hatsari a bincikena, hakika na kara yadda da lamarin gwamna Zulum, rayuwarsa ya sadaukar saboda al'ummarsa.

Northeast Reporters sukace da ya ziyarci garin a yau, ya zagaya wasu gine ginen gwamnati da na al'ummah wanda suka hada da sakatariyan karamar hukuma, babban asibiti, makarantu da sauransu wanda duk 'yan ta'addan sun lalata, gwamnan yayi alkawarin cewa zai sake gina garin da iznin Allah.

Ba da jimawa ba, sojojin kundunbala na Nigeria, da rundinar kasashen dake iyaka da yankin tafkin Chadi (MN/JTF) suka kwato garin na Marte.

Ba da jimawa ba yayi wata maganar da ta ja hankalin duniya; yace wadannan yara 'yan ta'addan Boko Haram an san inda suke, shugabannin gwamnati da na gargajiya da makamantansu sun san inda suke saura ayi abinda ya dace wajen dakile su.

Muna rokon Allah Ya tsare gwamna Babagana Zulum, Allah Ya cika masa burinsa na kawo karshen ta'addancin Boko Haram da masu tallafa musu.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment