Monday, 2 December 2019

Gwamnan Borno ya baiwa kananan 'yan kasuwa Tallafin jari

Maigirma gwamnan jihar Borno kuma Buharin Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya fara gabatar da tsarinsa na tallafawa kananun 'yan kasuwa da masu sana'ar hannu a yau Lahadi
Akwai kananun 'yan kasuwa mutum dari biyar da talatin da uku (533) daga yankin Shehuri-North sun samu tallafi na Naira dubu dari biyu (200,000), wasu Naira dubu dari daya (100,000) wasu kuma naira dubu talatin (30,000)

Burin gwamna Zulum shine ya taimakawa talakawa gajiyayyu da 'dan jari su fara karamar sana'a da zasu dogara da ita

Masu karin magana sukace wata miya mai dadi sai a makwabta, gwamna Zulum kuma Buharin Borno Allah Ya kara maka taimako.
Daga Datti AssalafiyKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment