Sunday, 1 December 2019

Gwamnan Jahar Kebbi Sanata Bagudu Ya Mika Yaron Da Aka Sace Ga Iyayensa

Gwamnan jahar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya mika yaron da aka sace hannun iyayen shi bayan kwashe watanni uku hannu masu satar yara.An bayyana sunan yaron da Silantaneme daga iyalan Dazi Kaka Shadawanka dake yankin Zuru a jihar Kebbi.

Gwamnan Bagudu ya mika yaron ga iyayenshi gaban shugaban karamar Hukumar Zuru, Daraktan Hukumar DSS na jahar Kebbi, da kuma 'yan jaridu.

Satar yara dai ya fara mamayar jahar kebbi.

Sai dai a irin wannan matakai da Gwamnati ke dauka za su taimaka sosai wurin shawo kan wannan matsala.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment