Wednesday, 4 December 2019

Gwamnatin jihar Kano bata kwacewa Sarkin Kano Fili ba

Hukumar da ke kula da filaye ta jihar Kano ta yi watsi da wasu rahotanni da ke cewa gwamnatin jihar ta kwace filin Sarki Muhammadu Sanusi wanda aka kimanta kudinsa ya kai Naira miliyan 250 kuma a cewar rahotannin an biya Sarkin diyyar Naira miliyan 4.5.


A wata sanarwa da kakakin hukumar, Murtala Shehu Umar ya fitar ya ce gwamnatin jihar ba ta kwace filin Sarkin ba.

Ya kuma ce duk da cewa gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na gina babbar gada, irinta ta farko a kasar, kuma saboda yanayin tsarinta da girmanta za a rusa wasu gine-gine a kusa da ita.

Cikin gine-gine da aka rusa har da wata katanaga da ta kewaye filin sarkin kuma da saninsa da izininsa aka rusa katangar, amma ba a taba filin ba.

Sanarwar kuma ta bukaci Sarkin da ya aika wa hukumar lambar asusun ajiyarsa ta banki don gaggawar biyansa diyyar katangarsa.
BBChausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment