Tuesday, 3 December 2019

Idan dokar kalaman batanci ta tabbata da uwargidan shugaban kasa zata fara>>Inji Farooq Kperogi

Sanannen dan jaridarnan kuma malamin Jami'a a kasar Amurka daya shahara wajan caccakar gwamnati, Farooq Kperogi ya bayyana cewa idan aka saka dokar kalaman kiyayya cikin doka to da matar shugaban kasa,Hajiya A'isha Buhari zata fara.Ya kafa hujja ne da cewa sanatan da ya kawo wannan kuduri, Muhammad Sani Musa a hirar da yayi da gidan talabijin na kasa kan dalilin da yasa ya kawo wannan kudiri ya bayyana cewa, yada jita-jitar maganar auren shugaban kasar Muhammadu Buhari da ministar kula da ibtila'i, Tallafawa al'umma Sa'diya Faruq Umar.

Yace to idan dai za'a hukunta wadanda suka kawo wancan labari to dole a fara ta kan iwargidan shugaban kasa Saboda a cewarshi a hirar da A'ishar ta yi da BBC ta tabbatar da maganar auren a kaikaice inda tace "Wacce aka ace Buhari zai aura ba ta yi zaton ba za a yi auren ba"

Ya kara da cewa na kusa da A'isha Buhari sun gayamai cewa, hadiman ta ne suka kara ruruta wutar kace-nace da aka rika yi a shafukan sada zumunta dan a lalata maganar auren.

Hakanan Farooq ya zargi sanata Musa da cewa shine aka hukumar zabe ta baiwa Kamfaninshi kwagilar kawo na'urar tantance masu zabe a shekarar 2015 wanda kuma akwai alamar tambaya akan aikin.

Farooq Kperogi yayi wannan bayanine a shafinshi na farooqkperogi.comKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment