Monday, 2 December 2019

Inyamurai Masu fafutukar kafa kasar Biafra sun kase 'yansanda 2 tare da kone motarsu

Hukumar 'yansandan jihar Anambra ta tabbatar da kashe jami'anta guda 2 da konr gawarsu da motar aikinsu da inyamurai masu fafutukar kafa kasar Biafra,IPOB suka yi a yau Litinin.Kakakin 'yansandan Jihar, Haruna Muhammad ne ya tabbatar da wannan batuninda yace jami'ansu sun sunje kama wani Lauya da aka kawo musu korafi akanshi na yin karfa-karfa kan wani fili sannan an aikamai da sakon gayyatar 'yansanda amma yaki zuwa.


Yace jami'an 'yansandan na isa kofar gidan Lauyan sai 'yan kungiyar ta Ipob suka rufar musu da makamai kala-kala inda aka jiwa wasu rauni har jami'ai 2 suka rasu.

Yace wadanda suka ji rauni suna Asibiti sannan an sake kai jami'an tsaro yankin na sojoji da 'yansanda dan kiyaye doka da oda sannan kuma an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.

hakanan shima shugaban kungiyar ta Ipob, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kai samame gidan lauyanshi ayau inda suka kashe wasu mabiyan kungiyar inda yayi Allah wadai da lamarin.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment