Monday, 2 December 2019

Kalli yanda Ronaldo ya hana Juventus cin kwallo a wasan suka buga 2-2 da Sassuolo

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta buga 2-2 da Sassuolo a wasan da suka buga daren jiya na gasar cin kofin Serie A.
Bonucci ne ya fara ciwa Juve kwallo inda Sassuolo ta farke ta ta kuma kara saidai an samu mugun daga kai Sai Gola wanda Ronaldo ya ci, wannan kwallon ta Ronaldo itace kwallonshi ta farko a cikin kusan wata daya daya shafe baya cin kwallo.

Ana kusa da tashine Dybala ya kai wani hari saidai Ronaldo bisa kuskure ya tare kwallon inda ya hanata wucewa da kafarshi, wannan abu ya dauki hankula.

Haka aka tashi wasan 2-2 wanda sanadin haka Juventus ta dawo matsayi na 2 inda Inter Milan da tawa Spal ci 2-1 ta dare saman teburin Serie A inda ta baiwa Juve tazarar maki 1 tal.

Saidai duk da wannan har yanzu Juventus bata yi rashin nasara a wasanninta na kakar wasan bana ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment