Sunday, 1 December 2019

Karamin Yaron Da Yake Amfani Da Goran Madara Yana Kirkirar Fitila Mai Hasken Awa Biyar

FASAHA:
Wannan shine 'Dalibi Ibrahim Yakubu Muhammad, mazaunin garin Rinjin Gani daga karamar hukumar Toro jihar Bauchi.


Ibrahim mai shekaru 17 a duniya, yana matakin aji 3 a babbar makarantar sakandire a Makrantar GC Toro.

Ibraheem, yana amfani da Goran abin sha na "Dudu Nutri Milk" wajan yin fitila da za ta bada haske na tsawon lokaci.

Fitilar tana yin caji na mintuna 30 kacal sannan ta yi aikin awowi biyar, tana tattare da sifika na sauti tare da wajen cajin waya ko karamar fanka.

Wannan wata babbar dama ce na bude kwakwlawa matasan zuwa babban mataki, a irin wannan lokaci da duniya take alfahari da kirkire-kirkire da cigaban zamani. 

Allah ya kara basira da kaifin kwakwalwa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment