Tuesday, 3 December 2019

Karin Haske kan dokar Kalaman Batanci: Babu wanda zai kamaka dan ka zagi masu rike da mukaman gwamnati ko dan ka soki gwamnati>>Minista

Karamin ministan kwadago wanda kuma lauyane, Festus Keyamo ya tabbatar da goyon bayanshi kan dokar kalaman batanci da majalisar tarayya ke kokarin sakawa cikin doka wadda kuma ta dauki hankulan mutane sosai a ciki da wajen Najeriya.
Keyamo ya bayyana hakane a shafinshi na Twitter inda yace babu wanda zai yadda da hukuncin kisa kan wanda yayi kalaman batanci amma mutum bazai tashi kawai ya saka labaran karya da zasu iya kawo tashin hankali ba ace za'a kyaleshi, dole a hukubtashi.

Yace bari yayi karin haske akan dokar, babu wanda zai kamaka dan ka zagi shugaban siyasa ko kuma dan ka soki gwamnati amma kada ka kirkiro karyar da zata tada hankula wannan dolene a hukuntaka.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment