Friday, 13 December 2019

KIRAN BUHARI DA 'DAN KAMA KAYRA' Tambayoyi 20 Ga Jaridar 'The Punch'

An fassara wasu sashi ne daga asalin rubutun da aka yi da harshen Turanci.

Tunda dai kuna ganin kama Omoyele Sowore da Hukumar DSS ta yi sakamakon laifukan da ake zarginsa da aikatawa na yinkurin kifar da Gwamnati, hakan shine ya sa za ku kira Shugaba Buhari da sunan mai mulkin kama karya.


1.. A watan Yuni na shekarar 2014, Sojoji tare sa jami'an tsaron DSS dauke da manyan makamai sun dira a ofisoshin Jaridun PUNCH, DAILY TRUST da LEADERSHIP suka kulle su gaba daya har sama da sati guda ba su samu damar aiki ba, to da a ce a lokacin mulkin Shugaba Buhari hakan ya faru, da wanne suna za ku kira shi kenan?

2.. A mulkin siyasa da muke yi a Nijeriya, an samu shugaban kasar da ya saka idanu ya bari 'yan Majalisar jiha guda biyar suka tsige Gwamna, sannan wasu 'yan Majalisar guda bakwai suma suka tsige Gwamna kawai saboda Gwamnonin ba sa jituwa da shugabannin dake mulki a shekarar 2001 zuwa 2014, da Shugaba Buhari ne ya yi haka me za ku ce ya yi wa tsarin siyasar Nijeriya kenan?

3.. Ko sau daya shugaba Buhari bai taba yinkurin tsige shugaban Majalisar Dattawa ko kakakin  Majalisa ba, ku Punch kuna ina lokacin da shugaba a Nijeriya ya yi amfani da mulki tare da kudi ya tsige shugabannin Majalisar Dattawa tare da kakaki kawai saboda ba su amince da tsarin sa na sin zuciya ba, da wanne suna kuka kira shi wannan shugaban da ya aikata haka, ko kuwa saboda shi ba tsohon soja bane kuke so ku ce?

4... Na san dai kuna nan lokacin da shugaba Jonathan ya sa aka rufe ofishin da (nPDP) suka bude a shekarar 2014, wanda ke Maitama Abuja, kuma dai ai kun san cewa Shugaba Buhari bai aikata irin haka ba lokacin da wasu 'yan jam'iyyar APC suka samar da rAPC bai kulle musu ofis ba, bai sa an kama su ba, bai ci zarafin su ba, shin da wanne suna kuka kira Shugaba Jonathan shi kuma?

5.. Ina fatan dai ba ku manta lokacin da wani shugaba ya tura DPO na hukumar 'yan sanda zuwa cikin gidan da Gwamnoni ke taron su na nPDP ba a Abuja, duk da cewa ba su karya dokar kasa ba kuma suna da kariya a tare da su, amma a hakan shugaban ya tura musu DPO ya wulakanta su tare da daukar bidiyon da aka dinga yadawa a duniya, shin da wanne suna kuka kira shugaban da ya aikata haka, ko kuwa dai kun rena Muhammadu Buhari ne shi?

6.. A nan Nijeriya aka samu shugaban da ya hana jirgin sama sauka a wata jiha, kawai saboda jirgin yana dauke da Gwamnan da ba ya tare da shugaban kasa, hakan fa ya faru a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014, shin da a ce shugaba Buhari ne ya aikata haka, wanne suna za ku saka masa kenan?

7.. A lokacin da za a gudanar da zaben Gwamna a jihar Ekiti a shekarar 2014, Rotimi Ameachi na jam'iyyar APC ya jagoranci tawagar mutanen APC zuwa jihar domin saka idanu akan zaben, amma aka saka sojoji suka hana shi da tawagarsa shiga jihar, kuma a lokacin aka bawa sauran Gwamnoni na Jam'iyyar PDP izinin shiga jihar. Da Buhari ne ya aikata haka me za ku ce kenan?

8.. Shugaba Muhammadu Buhari bai taba sawa an janyewa wani zabebben dan siyasa jami'an tsaro ba, kawai saboda ya fice daga APC zuwa jam'iyyar adawa, amma ai a zamanin mulkin Obasanjo an aikata haka a shekarar 2002 da kuma zamanin mulkin Jonathan a shekarar 2014, shin duk wadannan ba laifukan da za ku kira shugabannin da mulkin kama karya ba, sai Shugaba Buhari za ku kira saboda kun rena shi?

9.. A shekarar 2013 zababbun Gwamnoni a Nijeriya sun gudanar da zaben shugabancin kungiyar Gwamnoni, amma sai shugaba Jonathan ya ki amincewa da wadanda suka samu nasara, ya dauki tsagin da aka kayar su sha shida ya dinga amfani da su, saboda biyan bukatar kansa, shin wannan na kama karya bane?

10.. Da a ce shugaba Buhari ne ya tura da Kwamishinan 'yan sanda zuwa jihar Rivers a yanzu, har kuma ya ba shi umarnin takurawa zabebben gwamnan jihar, wajen toshe masa hanyar fita daga gidan Gwamnati, kamar dai yadda aka yi a shekarar 2013, na san da tuni kun sakawa Buhari suna Adolf Hitler saboda kiyayya.

11.. Babu irin maganganun da Gwamna Fayose bai gayawa Shugaba Buhari ba, musammam akan sha'anin tsaro, amma ko kallo bai ishi Buhari ba, kuna ina lokacin da Shugaba Jonathan ya sa aka tsige Gwamna Murtala Nyako a shekarar 2013, kawai saboda ya danganta Jonathan da Boko Haram, shin wannan ba kama karya bane, kuma ba karya tsarin mulki bane?

12.. A nan Nijeriya ne fa aka samu shugaban da ya sanya aka tattaro masa 'yan majalisar jihar Nassarawa, aka ajiye su a otel dake Abuja aka ba su umarnin su tsige Gwamna Almakura, shin da a ce Shugaba Buhari ne ya sa aka yi wa Gwamna Fayose na Ekiti haka, me za ku ce kenan?

13.. Duk da dai ba a san ko su waye suka dinga kashe shugabannin adawa na siyasa ba a shekarar 2001 zuwa 2014, amma da a ce a zamanin mulkin Shugaba Buhari ne ake wayar gari a ga an kashe babban dan adawa da me zaku ce kenan?

14.. Haka kawai a shekarar 2013 aka tura jami'an hukumar DSS suka dira a ofishin jam'iyyar APC mai adawa a lokacin, suka kwashe mahimman takardu tare da kame ma'aikatan dake aiki a ofishin jam'iyyar, da a ce shugaba Buhari zai aikata haka ga jam'iyyar PDP a yanzu, da me za ku ce kenan?

15.. A Shekarar 2012 zamanin mulkin Jonathan, manyan mutane a Nijeriya sun fito domin gudanar da zanga-zangar zaman lafiya a garin Lagos, Wole Soyinka, Femi Falana, Itse Sagay tare da sauran manyan mutane ke jagorancin zanga zangar, amma aka tura jami'an tsaro suka tarwatsasu, da a ce Shugaba Buhari ne ya yi haka, da sai ku ce ya aikata halin Sojoji, amma bai yi ba, duk da haka kuke cewa za ku kira shi da mai mulkin kama karya.

16. An yi lokacin da Gwamnatin Tarayya zamanin mulkin Jonathan ta hana kowanne jirgin sama sauka a Airport din Maiduguri, hatta Gwamnan jihar ba shi da ikon haka, sai mutum daya kawai wanda yake da alaka da shugaban kasa Ali Modu Sharif shi kadai ne ke iya sauka da jirgi a Airport din, Shugaba Buhari bai aikata ko kwatankwacin irin haka ba.

17. A cikin 'yan siyasar daga shekarar 2001 zuwa 2014 an samu wanda ya taba tsara shugaban jam'iyyar PDP da bindiga ya tilasata shi ajiye mukaminsa, kuma ba abun da aka yi masa duk da fitowar labarin, shin da a yanzu ne zamanin shugaba Buhari aka yi hakan, da me za ku ce kenan?

18.. A shekarar 2004 shugaba Obasanjo ya dakatar da bawa jihar Lagos tare da kananan hukumomin jihar kudaden su daga asusun Gwamnatin Tarayya, kawai saboda burin biyan bukatar kansa, hatta kotu ta umarci Gwamnati ta bayar da kudaden amma ya yi kunnen uwar shegu da umarnin, shin da a ce shugaba Buhari ne ya aikata hakan, da shi ne za ku ce ya zama mai mulkin kama karya.

19.. A zamanin mulkin Jonathan aka yi lokacin da aka dauko manyan 'yan ta'adda Asari Dokubo tare sa Tompolo aka ajiye su a otel mai daraja sannan aka ba su damar cin zarafin duk wanda ba ya goyon bayan Gwamnati, a zahiri aka yi haka, ba tare da tsoro ko kunya ba, shin da ace Shugaba Buhari ne ya aikata abun da bai haka ba, na tabbata da tuni kun dade kuna aibata shi da mugwayen kalamai.

20. Da wanne suna za ku kira Shugaba Buhari da a ce shine ya umarci Hukumar DSS su garkame zauren majalisa tare da cilla barkonon tsohuwa ga 'yan Majalisar da suka yi yinkurin shiga Majalisar, kuma an yi hakan ne don wai a kame kakaki Majalisar, haba Jaridar Punch me ya sa baku da adalci ne?

Cikekken rashin adalci ne jaridar Punch ta ce za ta danganta shugaba Buhari da mulkin kama karya, amma suka tsuke bakinsu akan shugabannin baya da suka yi kama karya na zahiri, wanda duk ma'abocin tarihi ya sani kuma ya gani.

Omoyele Sowore shine ya janyowa kansa aikata laifin da babu yadda za a yi jami'an tsaro su zuba masa idanu, a baya da yake adawa da Gwamnatin ba a kama shi ba, yanzu ma yinkurin kifar da kasa da ya yi shine dalilin da ya sa ake kama shi, kuma ma ai kotu ake kaishi wqjen sharia, ba wai ajiye shi aka yi ba tare da shari'a ba.
Daga Rabiu Biyora.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment