Monday, 2 December 2019

Kotu ta mikawa gwamnatin tarayya mallakin gidajen Saraki 2 dake Kwara

Babbar kotun gwamnatin tarayya dake Legas ta amincewa hukumar hana rashawa da cin hanci,EFCC ta gwace gidaje 2 na tsohon kakakin majalisar Dattijai kuma tsohon gwnan jihar Kwara.
EFCC tace a lokacin saraki yana gwamnan jihar Kwara daga shwkarar 2003 zuwa 2011 an yi zargin wani na hannun damarshi da kwashe wasu makudan kudi da suka kai Naira Miliyan 100 daga lokaci zuwa lokaci daga Asusun jihar.

EFCC ta bayyana cewa tana zargin da kudin haram dinne Saraki ya sayi wadancan gidaje.

Kotu ta bayar da damar mikawa gwamnatin tarayya gidajen na Saraki na wucin gadi inda ta bayar da nan da 17 ga watan Disamba ga duk wanda yake da wata kwakkwarar hujja ta hana a baiwa gwamnati gidajen na dindindin ya zo ya fada.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment