Sunday, 1 December 2019

Kyaftin Din Soja Kuma Hadimin Musulunci Ya Gamu Da Ajalinsa A Kan Hanyar Zuwa Jana'izar Mahaifinsa

Kamar yadda Abdurrazak Kabir Hizkil ya bayyana, yace wannan shine Kyaftin Ibrahim Rimi, Allah Ya karbi rayuwarsa a yau sakamakon hatsarin mota, an sanar dashi rasuwar mahaifinsa ya kama hanya zai tafi shima Allah Ya karbi abinsa.


Waye Kyaftin Ibrahim Rimi?
Yana da shaidar kwalin karatun digiri biyu akan ilmin addinin Musulunci (Islamic), kuma yanzu haka yana karatun digiri na uku (PhD) a Kasar Sudan.

Wallahi ni dai ban taba ganin sojan da yabawa addini lokacin sa ba kamar wannan, inji Abdulrazak

Kwanakin baya nafita harkar da’awa a jihar Akwa-Ibom, tare dashi mu ke ta yawo wuri wuri, har wajen garin Akwa-Ibom, nayi ta mamakin wai ya akayi Mutumin nan ya san da musulmai a wannan lungunan?, har ya shirya muhadarar da zan gabatar a barikinsa Ibawa Barrack 

Shekaran jiya kawai ina kwance a Portharcourt, sai naga video call ta WhatsApp dina, ina dubawa sai naga Kyaftin Ibrahim Rimi ne ya ke ta tilawar Qur’ani, nace akramakallahu anata tilawane?
Yace min Wallahi yana zaune ya tuno dani yakirani mugaisa, yace min anturashi course Lagos, zaiyi wata uku, amman ya kusa dawowa, nace to Malam kana dawowa ka kirani.
Kwatsam yau naji ankirani ancemin Allah Ya yiwa Kyaftin Rimi rasuwa. -Abdurrazak Kabir Hizkil

Muna rokon Allah Ya gafarta masa tare da mahaifinsa, Ya kyautata makwancinsu, muna mika sakon ta'aziyya ga iyalansu, Allah Ya basu hakurin jure wannan rashi mai taba zuciya.

Daga Datti AssalafiyKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment